Alakar Diplomasiyya Tsakanin Masar Da Sudan Na Ci Gaba Da Tsami
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i27285-alakar_diplomasiyya_tsakanin_masar_da_sudan_na_ci_gaba_da_tsami
Gwamnatin kasar Sudan ta bayyana cewar akwai yiyuwar ta dau wasu matakai masu tsauri kan kasar Masar a nan gaba, a ci gaba da kai ruwa da ke gudana tsakanin kasashen biyu.
(last modified 2019-01-16T04:00:45+00:00 )
Jan 15, 2018 02:21 UTC
  • Alakar Diplomasiyya Tsakanin Masar Da Sudan Na Ci Gaba Da Tsami

Gwamnatin kasar Sudan ta bayyana cewar akwai yiyuwar ta dau wasu matakai masu tsauri kan kasar Masar a nan gaba, a ci gaba da kai ruwa da ke gudana tsakanin kasashen biyu.

Jaridar Al-Sharq al-Awsat ta jiyo Abdel Mahmood Abdel Halim, jakadan kasar Sudan din a Masar wanda cikin 'yan kwanakin nan ya bar kasar Masar don komawa gida yana fadin cewa akwai yiyuwa a nan gaba gwamnatin Sudan ta dau wasu tsauraran matakai kan kasar Masar din.

Jakadan wanda yake jawabi a gaban 'yan jarida da wasu jami'an kasar ta Sudan da birnin Khartoum ya ce kiransa gida da aka yi wata alama ce da ke nuna cewa alakar da ke tsakanin kasashen biyu tana kara tsami.

Alakar diplomasiyya tsakanin Masar da Sudan din ta fara tsami ne sakamakon sabanin da suke da shi kan wasu yankuna guda uku da suke kan iyakokin kasashen biyu da kuma zargin da Sudan din take yi wa gwamnatin Masar na goyon bayan 'yan tawayen yankin Darfur ne.