An Jaddada Bukatar Yiwa Shugaban Harka Islamiyya A Nigeria Jinya Da Gaggawa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i27313-an_jaddada_bukatar_yiwa_shugaban_harka_islamiyya_a_nigeria_jinya_da_gaggawa
Shugaban dandalin yada labarai na harka Islamiyya a Nigeria Ibrahim Musa ya jaddada bukatar a gaggauta yi wa shugaban harkar magani.
(last modified 2018-08-22T07:01:17+00:00 )
Jan 16, 2018 02:56 UTC
  • An Jaddada Bukatar Yiwa Shugaban Harka Islamiyya A Nigeria Jinya Da Gaggawa

Shugaban dandalin yada labarai na harka Islamiyya a Nigeria Ibrahim Musa ya jaddada bukatar a gaggauta yi wa shugaban harkar magani.

Kamfanin dillancin labaran Mehr na kasar Iran ya nakalto Ibrahim Musa yana fadar haka a jiya Litinin, ya kuma kara da cewa yanayin rashin lafiyar shugaban harkar Sheikh Ibrahim Zakzaky abu ne mai tada hankali, don haka akwai bukatar ya sami ganin kwararrun likitoci don yi masa magana.

Ibrahim Musa ya kara da cewa, bayyanar shugaban harkar a ranar lahadin da ta gabata a gaban yan jiridu bai wadatar ba, sannan harkar ba za ta yi kasa a gwiwa ba domin ganin a sake shi, daga tsarewar da ake yi masa tun shekara ta 2015.