Afirka Ta Kudu Ta Kira Jakadan Amurka
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i27323-afirka_ta_kudu_ta_kira_jakadan_amurka
Ma'aikatar harakokin wajen Afirka ta kudu ta kira jakadan Amurka dake cikin kasar domin bayyana masa rashin jin dadi kan kalaman wulakanci da Shugaban Amurka ya yi ga kasashen Afirka.
(last modified 2018-08-22T07:01:17+00:00 )
Jan 16, 2018 08:49 UTC
  • Afirka Ta Kudu Ta Kira Jakadan Amurka

Ma'aikatar harakokin wajen Afirka ta kudu ta kira jakadan Amurka dake cikin kasar domin bayyana masa rashin jin dadi kan kalaman wulakanci da Shugaban Amurka ya yi ga kasashen Afirka.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya habarta cewa ma'aikatar harakokin wajen kasar Afirka ta kudu ta bi sahun wasu kasashen Afirka inda ta kira jakadan Amurka dake cikin kasar domin neman karin bayani kan furucin shugaban Amurka na cin zarafi da wulakaci ga kasashen Afirka.

Ma'aikatar harakokin wajen Afirka ta kudu ta aike da takardar nuna rashin amincewa  kan kalaman batancin da Shugaba Trump ya yi ga kasashen Afirka ga Jakadan kasar Amurka dake birnin Pretoria kafin ta kira shi zuwa babban ginin ma'aikatar.

Kafin haka ma gwamnatocin kasashen Senegal, Boswana, Najeriya da wasu kungiyoyin kasa da kasa wadanda suka hada da tarayyar Afrika duk sun yi Allah wadai da kalaman cin zarafi da shugabaTrump ya yi  a ranar Alhamis da ta gabata, inda ya kira wasu kasashe Afrika da suna "shara" ya kuma bukaci a hana mutanen wadannan kasashe shiga kasar ta Amurka.