Akwai Fargabar Ayyukan Ta'addanci Na Kungiyar ISIS A Afirka
Wata Jaridar Kasar Aljeriya ta habarta cewa akwai yiyuwar kai harin ta'addanci na kungiyar Da'esh a Kasashen Afirka
Jaridar Alhabar ta kasar Aljeriya ta habarta cewa akalla akwai mayakan Da'esh 400 a kasashen Libiya, Nijer da Mali a yankunan dake kan iyakoki da kasar Aljeriya, kuma bisa binciken da ma'aikatar leken asirin kasar ta yi akwai yiyuwar mayakan na ISIS suka kai gagarumin harin ta'addanci a mako mai zuwa.
Rahoton ya ce mataimakin ministan tsaron kasar Aljeriya Gaid Salah ya gana da manyan kwamandojin kan iyakar kasar, inda suka tattauna kan barazanar mayakan na ISIS dake yankunan dake kan iyakoki da kasar.
Bayan kashin da kungiyar ISIS din ta sha a kasashen Siriya da Iraki, mayakan kungiyar sun wasu a sassa daban daban na Duniya cikin kuwa har da kasashen Afirka.