Yan Bindiga Sun Sace Ba'amurke Guda Da Kuma Dan Canada A Nigeria
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i27393-yan_bindiga_sun_sace_ba'amurke_guda_da_kuma_dan_canada_a_nigeria
Yan bindiga sun sace wani ba Amurke da kuma dan kasar Canada guda a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja a tarayyar Nigeria
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
Jan 18, 2018 15:30 UTC
  • Yan Bindiga Sun Sace Ba'amurke Guda Da Kuma Dan Canada  A Nigeria

Yan bindiga sun sace wani ba Amurke da kuma dan kasar Canada guda a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja a tarayyar Nigeria

Shafin yanar gizo na Sahara reporters ya bayyana cewa satar ta auku ne a ranar talatan da ta gabata. Labarin ya kuma kara kara da cewa yan bindigan sun kashe yansanda biyu da suke rakiyar turawan a lokacin satar.

Satar yan kasashen waje da kuma yan siyasa ya zama ruwan dare a tarayyar Nigeri a cikin watannin da suka gabata a duk fadin kasar . Yan bindigan sun maida aikin satar mutane don karban kudaden fansa a matsayin sana'a. 

A wannan satar dai haryanzun ba'a ji doriyar mutanen ba, kuma babu wanda ya san abinda  masu satar suke nema. Satar yan kasashen waje da kuma kashesu a wasu lokata a tarayyar ta Nigeria ya fi yawaita  a yankin niger dalter saboda yawan ma'aikatan kamfanonin hakar man fetur a yankin. Barayin sukan  nemi diyya na kudaden fansa masu yawa kafin su sake wadanda suka kaman.