Madugun 'Yan Hamayyar Zimbabwe Ya Mutu A Wani Hatsarin Jirgin Sama
Madugun 'yan adawan kasar Zimbabwe da ke gudun hijira, Roy Bennett, tare da wasu mutane hudu sun mutu sakamakon wani hatsarin jirgin sama da ya ritsa da su a jihar New Mexico na Amurka.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar a wata sanarwa da jam'iyyar adawar ta fitar a jiya Alhamis ta ce Mr. Roy Bennett dan shekaru 60 a duniya ya mutu ne sakamakon hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu da ke dauke da shi tare da matarsa da wasu abokansa su uku a jihar ta New Mexico a ranar Larabar da ta gabata.
Mr. Roy Bennett wanda ya taba zama ma'ajin jam'iyyar adawa ta MDC, yana daga cikin fitattun 'yan siyasar kasar Zimbabwe wanda kuma ya shafe wani lokaci a gidan yari a lokacin mulkin tsohon shugaban kasar Zimbabwen Robert Mugabe saboda adawar da yake nunawa gwamnatin.
Mahukunta a Amurkan dai inda ya ke gudun hijira sun ce suna ci gaba da gudanar da bincike don gano musabbabin faruwar hatsarin.