'Yan Sanda Sun Kashe Mutane 5 A D/Congo
'Yan sanda a D/Congo sun halaka rayukan mutane biyar tare da jikkata wasu da dama na daban a zanga-zangar da aka gudanar ta adawa da Shugaban kasar.
A cikin wata sanarwar da wakilan MDD a jamhoriyar Dimokaradiyar Congon suka fitar sun ce 'yan sanda a Kinshasha babban birnin kasar sun kashe mutane akalla biyar tare da jikkata wasu da dama na daban a arangamar da suka yi da masu zanga-zangar neman kawo karshen mulkin shugaba Joseph Kabila na Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.
Rahotanni na cewa wasu Kiristoci mabiya darikar Katholika da masu fafutukar neman canji ne suka kira zanga-zangar ta yau, inda ya zuwa yanzu aka tabbatar da mutuwar mutane biyar
Ko baya ga birnin Kinshashan an gudanar da irin wannan zanga-zangar a biranan Goma da Lubumbashi, inda aka tabbatar da fitowar dubun dubatan mutane
A ranar 31 ga watan Disambar shekarar da ta gabata ma, an gudanar da gagarumar zanga-zanga ta neman shugaba Joseph Kabila ya sauka daga kan karagar milki, inda 'yan sandan kasar suka kashe mutane bakwai.