George Weah, Sabon Shugaban Laberia
Jan 22, 2018 07:46 UTC
A kasar Liberia yau Litini ne tauraron dan kwallon kafana duniya, George Weah, ke rantsuwar kama aiki a matsayin sabon shugaban kasar.
Daga cikin masu halartar bikin rabtsar da Weah har da shahararun 'yan wasa da suka hada da Didier Drogba da kuma Samuel Eto.
Mista Weah, zai gaji Madam Ellen Johnson Sirleaf, mace ta farko da ta zama zababbiyar shugabar kasa a nahiyar Afirka.
Masana dai na ganin da akwai babban kalubale ga sabon shugaban kasar ta Liberia da ke fama da matsalolin tattalin arziki.
Tags