Gambiya Ta Kama Wasu Tsoffin Janar Din Gwamnatin Jammeh Bayan Dawowarsu Gida
(last modified Tue, 23 Jan 2018 05:14:41 GMT )
Jan 23, 2018 05:14 UTC
  • Gambiya Ta Kama Wasu Tsoffin Janar Din Gwamnatin Jammeh Bayan Dawowarsu Gida

Rundunar sojin kasar Gambiya ta sanar da kama wasu tsoffin Janar-Janar na tsohuwar gwamnatin Yahya Jammeh ta kasar bayan dawowarsu gida daga gudun hijirar da suka yi bayan kifar da tsohuwar gwamnatin.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar a rundunar sojin ta sanar da hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Litinin inda ta ce an kama tsoffin janar din wato Umpa Mendy, babban jami'i mai kula da lafiyar tsohon shugaba Jammeh da kuma Asumana Tamba tsohon kwamandan dakarun kare fadar shugaban kasar jim kadan bayan dawowarsu kasar Gambiyan a ranar Lahadin da ta gabata, sannan kuma ana ci gaba da tsare su da kuma gudanar da bincike kansu.

Sanarwar ta ce an kama mutanen biyu ne a gidanjensu sai dai kuma ba ta yi karin bayani dangane da dalilinsu na dawowa gida din da kuma dalilin tsare su da aka yi ba. An jima dai ana jan kunnen sabuwar gwamnatin Gambiya da cewa wasu tsoffin jami'an sojin kasar da suke gudun hijira a waje suna iya zama barazana gare ta.

Kimanin shekara guda kenan aka rantsar da sabon shugaban kasar Adama Barrow, bayan da tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh ya gudu ya bar kasar sakamakon matsin lambar da ya fuskanta daga kasashen Yammacin Afirka na ya sauka daga karagar mulki bayan kayen da ya sha a zaben shugaban kasar da aka gudanar inda ya tafi kasar Equatorial Guinea.