AU Za Ta Kaddamar Da Shekara Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa
Jan 23, 2018 07:48 UTC
Kungiyar tarayya Afrika ta AU za ta kaddamar a hukumance da shekara nahiyar ta yaki da cin hanci da rashawa.
An kaddamar da shirin ne a yayin taron kungiyar karo na 30 da aka fara a ranakun 22 zuwa 29 na watan nan a Birnin Adis Ababa na kasar Habasha.
Shugaban hukumar zartarwar ta kungiyar tne Musa Faki Mahamat ya sanar da hakan a yayin bude zaman taron wakilan din-din-din na kungiyar PRC) karo na 35 a kasar Habasha.
A cewar shugaban, taken taron kolin kungiyar na wannan karo, shi ne, "yaki da cin hanci da rashawa: hanya mai dorewa ta farfado da nahiyar Afirka".
Tags