Benin : An Yi Zanga zangar Kin Jinin Salon Mulkin Shugaba Talon
Jan 24, 2018 07:41 UTC
A Benin dubban 'yan kasar ne suka gudanar da zanga-zanagr kin jinin salon mulkin shugaban kasar Patrice Talon.
Bayanai daga kasar sun ce kimanin mutane 20,000 suka shiga zanga-zangar da kungiyoyin farar hula da 'yan adawa suka kira duk da haramta zanga zangar da gwamnati ta yi.
Masu zanga zangar dai na raira taken la'antar gwamnati kan rashin tabuka wa talakawan kasar komai, tare da kira ga gwamnati da ta kira babban taron jin ra'ayi al'aumma kasar.
Tags