Sojojin Masar Sun Yi Wa Abdulfattah al-Sisy Mubaya
Jaridar 'Ra'ayul-Yaum' ta Masar wacce ta dauki labarin ta ce; Kame dan takarar shugaban kasa Janar Sami Adnan da aka yi, yana nufin amincewar sojoji kasar da ci gaba da mulki Abdulfattah al-Sisy.
Jaridar ta ci gaba da cewa; An tuhumi Janar Adnan mai ritaya da tunzura sojojin kasar, da keta dokokin soja, da kuma aikata manyan laifuka, wanda hakan yake nufin cewa zaben da za a yi a watan Maris na wannan shekarar yana nufin Sisi ne zai lashe, kamar yadda Husni Mubarak ya rika yi.
Jaridar ta kuma bayyana matakin da sojojin suka dauka a matsayin yi wa Abdulfattah al-Sisy mubaya'a.
Har ila yau jaridar ta ci gaba da cewa; Sojojin Masar ba su yi amanna da tsarin Demokradiyya ba, kuma sauran 'yan takarar shugaban kasa 6 sun fahimci haka, don haka suka fara janyewa.