Sudan Ta Kudu : Za'a Jibge Sojoji Don Yaki Da Sace-sacen Mutane
Jan 25, 2018 10:17 UTC
Kasar Sudan ta Kudu ta yunkuri anniyar jibge sojiji don yaki da sace sacen yara da dabbobi dake ci gaba da karuwa tsakanin kabilu dake yakar juna.
Matsalar sace sacen mutane musamen yara na dada karuwa tsakanin kabuku a yankin arewacin wannan kasa ta Sudan ta Kudu da yaki ya daidaita.
Mataimakin shugaban kasar Taban Deng ya fadawa manema labarai a Juba cewa nan gaba sojojin kasar na (SPLA) zasu fara aiki da mayan makamai da kayan aiki na soja kan kabilun dake wannan harka musamen 'yan kabilar Murles a yankin Pibor dake iyaka da kasar Habasha wadanda suka jima suna aikata wannan aika aika kan makobtansu 'yan kabilar Dinka.
Tags