Dangantakar Sudan Da Masar Ta Fara Kyautata A Taron Addis Ababa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i27709-dangantakar_sudan_da_masar_ta_fara_kyautata_a_taron_addis_ababa
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sudan ta bada labarin kyautatuwar dangantakar kasar da kasar Masar a taron da shuwagabannin Afrika suke gudanarwa a halin yanzu a kasar Ethiopia.
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
Jan 28, 2018 08:35 UTC
  • Dangantakar Sudan Da Masar Ta Fara Kyautata A Taron Addis Ababa

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sudan ta bada labarin kyautatuwar dangantakar kasar da kasar Masar a taron da shuwagabannin Afrika suke gudanarwa a halin yanzu a kasar Ethiopia.

Kamfanin dillancin labaran Spoting  ya nakalto labarin cewa shuwagabannin kasashen Biyu sun gana da juna a birnin Adis Ababa inda suka amince da kafa wani kwamiti wanda zai kunshi wakilan kasashen biyu don tattauna hanyoyin warware sabanin da ke tasowa tsakanin kasashen biyu. 

Kamfanin dillancin labaran SUNA na kasar Sudan ya bayyana cewa sabani na baya-bayan nan tsakanin kasashen biyu ya taso ne kan ginin madatsar ruwa ta Annahdah a cikin kasar Ethiopia. 

A yau ne aka fara taron shuwagabannin kasashen Afrika karo na 30 a birnin Adis ababa na kasar Ethiopia.