An Jefa Tshon Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Masar A Cikin Kurkuku
(last modified Sun, 28 Jan 2018 12:08:31 GMT )
Jan 28, 2018 12:08 UTC
  • An Jefa Tshon Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Masar A Cikin Kurkuku

Lauyan Tsohon babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Masar wanda ya bayyana anniyarsa ta shiga takarar shugabancin kasa, ya ce an ba shi dama ya gana da tsohon shugaban sojojin a gidan yari .

Jaridar ra'ayul yaum kasar Masar ta nakalto a cikin shafinta na internet kan cewa Nasir Amin lauyan Sami Anan ya ce ya sami ganinsa a gidan yari, kuma ana zarginsa da saba wa tsaron tafiyar da harkokin sojoji a kasar, sannan tare da yin amfani da takardun aikin soji domin shiga harkokin da ya shafe shi shi kadai.

Kafin nan dai, Ahmad shafiq tsohon Priministan kasar ma ya bayyana janyewarsa daga takarar shugabancin kasar. Har'ila yau Khalid Ali wani dan takarar neman kujerar shugabancin kasar ta Masar shi ma ya bayyana janyewarsa.