An Bude Taron Koli Na Kungiyar AU Karo Na 30
An bude taron koli na kungiyar tarayya Afrika karo na 30 a birnin Adis Ababa na kasar Habasha.
Taron wanda akawa taken '' yaki da cin hanci da rashawa, hanya mai dorewa ta farfado da nahiyar Afirka", zai maida hankali kan mahimman abubuwa guda biyar da suka hada da yaki da ta'addanci da karfafa alaka tsakanin kasashen nahiyar da yaki da cin hanci da rashawa.
A yau Lahadi shugabannin kasashe mambobin kungiyar sun tattauna a daura da taron kan wani shiri na yi wa tsarin kungiyar kwaskwarima ta yadda zata dogoro da kanta, maimaikon dogoro da kasashen turai ko Amurka ko Japon.
Daga cikin baki da suka halarci taron har da babban sakatare na MDD, Antonio Guterres, da sakatare Janar na kungiyar kasashen larabawa, Ahmed Abou el-Gheit, da kuma shugaban Palastinawa Mahmoud Abbas.
Shugaba Mahamadu Buhari na Najeriya, da takwaransa na Sudan ta Kudu, Salva Kiir wadanda basu samu damar halartar taron da ya gabata ba na halartar taron na wannan karo.
Shugaba Paul Kagame na Ruwanda ne zai karbi shugabacin karba karba na kungiyar a hannun takwaransa na Guinea Alfa Konde.