An Dage Dokar Hana Tarurrukan Siyasa A Kasar Gambia
Yan sanda a kasar Gambia sun bada sanarwar dage dokar hana tarurrukan siyasa a kasar bayan kafa wannan doka ne na tsawon kimanin makonni biyu .
Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya nakalto majiyar jami'an tsaron suna bada sanarwan haka a jiya Litinin.
Magoya bayan jam'iyyar shugaba Adama Barow da kuma na tsohon shugaban kasar Yahyah Jame sun yi ta rikici a tsakaninsu makonni biyu da suka gabata wanda ya tilastawa jami'an tsaron kasar hana dukkan tarurrukan siyasa a kasar.
Labarin ya kara da cewa duk wata Jam'iyyar siyasa wacce take son gudanar da taro dole ne ta gabatar da bukatar hakan a rubuce ga babbar cibiyar 'yan sanda a birnin Banjul.
A ranar 15 ga watan Janairun da muke cikin ne yan sanda a kasar ta Gambia suka dakatar da dukkanin harkokin siyasa sakamakon rigimar da ta jawo raunata wasu mutane a wani taron siyasa a kasar. A ranar 12 ga watan Afrilu mai zuwa ne za'a gudanar da zaben shugaban a kasar ta Gambia.