Sudan Ta Ki Amincewa Da Shawarar Masar Akan Madatsar Ruwan Habasha
Ministan makamashi na kasar Sudan Mu'utaz Musa ne ya bayyana watsin da kasarsa ta yi da shawarar kasar Masar, tare da cewa nan da wani lokaci za a sake bude tattaunawa kan lamarin
Mu'utaz ya kara da cewa kasar tasa ba ta yarda da a mayar da batun madatsar ruwan ta zama ta kasa da kasa ba ko kuma a shigar da Bankin duniya acikin lamarin.
A jiya litinin shugabannin kasashen Masar, Sudan da piraminstan Habasha suka yi ganawar bayan fage a birnin Adis Ababa inda suka tattauna batun madatsar ruwan.
Sudan tana goyon bayan gina madatsar ruwan da Habasha take yi, saboda zai amfane ta ta fuskar noman rani da kuma samun wutar lantarki. Sai dai Masar na daukar madatsar a matsayin barazana a gare ta saboda yiyuwar raguwar kwararar ruwan Maliya zuwa cikin kasar.