ECOWAS Ta Sanya Wa Guinea Bissau Takunkumi
Kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) ta sanar da fara aiwatar da takunkumi kan 'yan siyasa da kungiyoyin siyasar Guinea Bissau a hukumance, saboda Guinea Bissau din ta ki martaba yarjejeniyar birnin Conakry.
Tawagar ECOWAS din karkashin shugabancin ministan harkokin waje da hadin gwiwa na kasar Togo mista Robert Dussey ta sanar da hakan ne a birnin Bissau, fadar mulkin kasar ta Guinea Bissau.
Mr. Dussey ya ce, Guinea Bissau ba ta nada firaministan kasa wanda sassa daban daban suka amince da shi ba kamar yadda yarjejeniyar Conakry ta bukata.
Haka kuma gwamnatin ba ta biya bukatun gudanar da zaben 'yan majalisa, wanda zai bude kofa ga sassa daban daban, sai dai kuma Dussey bai fayyace tanade-tanaden da ke kunshe cikin takunkumin ba.
Har ila yau ECOWAS ta yi kira ga kungiyar tarayyar Afirka wato AU, da kungiyar hadin kan kasashe masu magana da harshen Portugal, da kungiyar tarayyar Turai wato EU, da MDD cikin gaggawa su ma su sanya wa Guinea Bissau takunkumi.