Gwamnatin Sudan Ta Kama Mataimakin Shugaban Babbar Jam'iyyar Adawa Ta Kasar
Jami'an tsaron kasar Sudan sun yi awun gaba da mataimakin shugaban babbar jam'iyyar adawa ta Umma Party ta kasar bayan zanga-zangar kin jinin gwamnatin da jam'iyyar ta shirya don nuna rashin amincewa tashin farashin kayayyakin abinci a kasar.
Jam'iyyar Umma din wacce take karkashin jagorancin tsohon firayi ministan kasar ta Sudan Sadiq al-Mahdi ce ta sanar da hakan cikin wata sanarwa da ta fitar inda ta ce jami'an hukumar leken asiri da tsaron kasa ta (NISS) ta kama da kuma tsare, Fadlalla Burma Nasir, mataimakin shugaban jam'iyyar bayan samamen da suka kai gidansa.
Jam'iyyar ta kara da cewa tana Allah wadai da kama babban jami'in nata wanda tsohon manjo janar ne na sojin Sudan din kana kuma tsohon ministan tsaro a gwamnatin ta Mahdi, inda ta bukaci da a gaggauta sako shi ko kuma gurfanar da shi a gaban kotu, kamar yadda kuma ta yi Allah wadai da ci gaba da kame mutane da gwamnatin take yi sakamakon zanga-zangar.
Tun a farko-farkon watan Janairun da ya gabata ne dai ake ta gudanar da zanga-zangogi a birnin Khartoum, babban birnin kasar ta Sudan da wasu garuruwa don nuna rashin amincewa da hauhawar farashin kayakkain abinci musamman biredi.