Gwamnatin Masar Ta Gudanar Da Garambawul A Hukumar Leken Asirin Kasar
Gwamnatin Masar ta sanar da tsige shugaban hukumar leken asirin kasar Khalid Fauzi daga kan mukaminsa tare da wasu manyan jami'an hukumar guda bakwai.
Shafin watsa labarai na Khalij Ajjadid ya habarta cewa: Shugaban kasar Masar Abdul-Fatah Al-Sisi ya sanar da tsige shugaban hukumar leken asirin kasar Khalid Fauzi daga kan mukaminsa tare da sanar da Abbas Kamil shugaban ofishinsa a matsayin mukaddashin hukumar kafin sanar da sabon shugabanta.
Har ila yau shugaban kasar ta Masar ya tsige manyan jami'an hukumar leken asirin guda bakwai daga kan mukamansu, inda wasu rahotonni ke bayyana cewa: Manyan jami'an hukumar leken asirin kasar ta Masar suna da alaka ta kud da kud da Sami Anan tsohon janar na rundunar sojin kasar da ya sanar da aniyar ta tsayawa takarar shugabancin kasar ta Masar da za a gudanar a watan Maris mai zuwa.
Tuni dai rundunar sojin Masar ta kame Sami Anan kan zargin neman raba kan rundunar sojin Masar tare da kokarin tunzura al'ummar kanta.