Cutar Ebola Ta Kashe Mutane biyar A Guinea
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i2794-cutar_ebola_ta_kashe_mutane_biyar_a_guinea
Hukumar yaki da cutar Ebola a kasar Guinea ta sanar da mutuwar mutane biyar sakamakon kamuwa da cutar Ebola bayan sake bullar ta a wannan kasa dake yammacin Afirka.
(last modified 2018-08-22T06:58:01+00:00 )
Mar 22, 2016 13:34 UTC
  • Cutar Ebola Ta Kashe Mutane biyar A Guinea

Hukumar yaki da cutar Ebola a kasar Guinea ta sanar da mutuwar mutane biyar sakamakon kamuwa da cutar Ebola bayan sake bullar ta a wannan kasa dake yammacin Afirka.

kanfanin dilancin labaren Faransa na AFP ya rawaito kakakin hukumar Fodé Tass Sylla na fadar cewa tun daga sake bullar cutar mutane biyar ne suka rasa rayukan su.

kazalika a cewar jami'in akwai wasu mutane 961 da ake kautata zaton sunyi mu'amula da wadanda mahaukaciyyar cutar ta kashe.

Wannan dai na zuwa ne ‘yan kwanaki kalilan da hukumar lafiya ta duniya WHO/OMS ta ce, babu sauran cutar a kasar Saliyo mai makwabtaka da Guinea.

An yi amanna cewa, cutar ta Ebola ta fara bulla ne a kasar Guinea yayin da ta kashe sama da mutane dubu 11,300 tun bayan barkewarta a shekarar 2013 a kasashen Liberia da Saliyo da Guinea.