Zazzabin Lasa Ya Hallaka Mutane 31 A Najeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i27963-zazzabin_lasa_ya_hallaka_mutane_31_a_najeriya
Ma'aikatar Kiyon Lafiya ta Najeriya ta sanar da billar cutar Lasa a kasar
(last modified 2018-08-22T07:01:23+00:00 )
Feb 06, 2018 02:08 UTC
  • Zazzabin Lasa Ya Hallaka Mutane 31 A Najeriya

Ma'aikatar Kiyon Lafiya ta Najeriya ta sanar da billar cutar Lasa a kasar

Majiyar Hukumar radio da talabijin ta kasar Iran ta nakalto Isaac Adewole ministan kiyon lafiyan Najeriya a wani taron gaggawa da ya kira a ofishinsa dake birnin Abuja a wannan Litinin na cewa zazzabin cutar lasa ya bulla a cikin jahohi 15 na kasar da ya zuwa yanzu ya yi sanadiyar mutuwar mutane 31 a kasar.

Adewole ya kara da cewa daga farkon shekara zuwa yanzu kimanin mutane 77 ne suka kamu da wannan cuta, sannan ya bukaci cibiyoyin bincike na kasar da su gaggauta gudanar da bincike domin gano dalilan da suka sanya wannan cuta ta sake bulla a Najeriya.

Sake bullar zazzabin wanda tun a shekarar 1969 ya fara bulla a garin Lassa da ke jihar Borno ya jawo sake fuskantar wata barazana a fannin kula da lafiya, domin daga jihohi biyu a yanzu zazzabi ya kai ga bulla a yanki Kudu maso Yammacin kasar, Sannan kuma ya sanya gwamnatin kara mikewa tsaye domin yi ma zazzabin na Lasa tarba-tarba ta hanyar kafa kwamitin kwararru don ya kai ziyara a jihohin da cutar tafi kamari na jihohin Niger, Kano da kuma Bauchi.

Ministan kula da lafiya na Najeriyar Farfesa Isaac Adewale da ya jagorancci taron musamman don bayyana hakikanin  halin da ake ciki, ya bayyana cewa matakan da ake dauka sun taimaka wajen shawo kan matsalar.