Rundunar 'Yan Sandan Nijeriya Tana Neman Kakakin Babangida Ruwa A Jallo
(last modified Tue, 06 Feb 2018 17:36:10 GMT )
Feb 06, 2018 17:36 UTC
  • Rundunar 'Yan Sandan Nijeriya Tana Neman Kakakin Babangida Ruwa A Jallo

Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta sanar da cewa tana neman kakakin tsohon shugaban kasar Janar Ibrahim Babangida (rtd), wato Kassim Afegbua, ruwa a jallo saboda fitar da sanarwar bogi da kuma bata suna abin da zai iya janyo rigima da tashin hankali a Nijeriyan.

Kakakin rundunar 'yan sandan, Jimoh Moshood, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a yau din nan Talata inda ya ce sufeto Janar na 'yan sandan Nijeriyan Ibrahim Idris ya ba da umurnin kamo Mr. Afegbua  saboda 'bayanan karya da ya fitar, bata suna da zai iya haifar da rigima da rikici a duk fadin kasar.

Kakakin 'yan sandan ya ce rundunar tana kiran kakakin Babangidan da ya kai kansa ofishin 'yan sandan da ya fi kusa da shi.

A ranar Lahadin da ta gabata ce Mr. Afegbua ya fitar da wata sanarwa da yake daga Janar Babangida din ce inda ya kirayi 'yan Nijeriya da kada su zabi shugaba Muhammadu Buhari a zaben da za a gudanar a 2019 da kuma kiran da a mika mulki ga matasa masu jini a jika. To sai dai a jiya Litinin Janar Babangidan ya musanta wannan sanarwar yana mai cewa ba da yawunsa aka fitar da ita ba.

Sanarwar bogen da Mr. Afegbua ya fitar ta zo ne kwanaki bayan wata wasika da tsohon shugaban Nijerian Olusegun Obasanjo ya rubuta inda ya kirayi shugaba Buharin da kada ya tsaya takarar shugabancin a zaben 2019 lamarin da har yanzu yake ci gaba da daukar hankula a kasar.