ECOWAS Ta Kakaba Wa Jami'an Guinea Bissau 19 Takunkumi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i27995-ecowas_ta_kakaba_wa_jami'an_guinea_bissau_19_takunkumi
Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS), ta kakaba wa wasu jami'an Guinea Bissau 19 da takunkumi, saboda kin martaba yarjejeniyar kawo karshen rikicin siyasar kasar.
(last modified 2018-08-22T07:01:23+00:00 )
Feb 07, 2018 01:49 UTC
  • ECOWAS Ta Kakaba Wa Jami'an Guinea Bissau 19 Takunkumi

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS), ta kakaba wa wasu jami'an Guinea Bissau 19 da takunkumi, saboda kin martaba yarjejeniyar kawo karshen rikicin siyasar kasar.

Takunkumin wanda ya shafi 'yan siyasa da 'yan majalisa ciki har da na kusa da shugaban kasar Jose Mario Vaz, ya tanadi toshe kudaden ajiyar mutanen da kuma haramta masu tafiye-tafiye a yankin.

Matakin dai ya biyo bayan kashedin da kungiyar ta ECOWAS ta yi ne, akan rikicin siyasar da yaki ci yaki cinyewa a wannan karamar kasa dake yammacin Afrika.

Rikicin siyasa a wannan kasa dai ya samo asali ne tun lokacin da shugaban kasar ya tsige firayi ministansa, Domingos Simoes Pereira, shugaban Jam'iyyar PAIGC mai mulki a kasar.

Tun a ranar daya ga watan nan ne ECOWAS ta sanar da takunkumin sai dai ba  tare da fayyace wadanne bangarori ko su wa ya shafa ba.