An kame mayakan Ashabab Da Dama A Somaliya
Dakarun tsaron Somaliya Sun sanar da kame mayakan kungiyar ta'addancin nan ta Ashabab da dama a kasar Somaliya
Kamfanin dillancin labaran Xin huwa na kasar China daga birnin Magadishu ya nakalto wani jami'in tsaro kasar Somaliya a jiya Assabar na cewa, bisa wani samame na hadin gwiwa da Sojojin kasar tare da Dakarun tsaro da sulhu na kasashen Afirka suka kai kauyen Jauhar, kimanin mayakan Ashabab 50 ne aka kame.
Kauyen Jauhar na da nisan kilomita 90 da Magadushu babban birnin kasar.
A bangare guda, kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya yi Alawadai kan harin ta'addancin da kungiyar Ashabab ta kai a makun da ya gabata, inda ya bukaci masu taimakawa kungiyar da su dakatar da taimakon kundaden da suke bata.
A makun da ya gabata ne kungiyar ta Ashabab ta kai wani mumanan harin ta'addanci a wani gurin cin abinci, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar Mutane akalla 20.
Kungiyar Ashabab ta Zamanto babbar bazana ga kasar Somaliya da ma kasashen dake makobtaka da ita.