Sudan Ta Kudu : An Yi Zanga-zangar Kin Jinin Amurka A Juba
(last modified Wed, 07 Feb 2018 05:20:44 GMT )
Feb 07, 2018 05:20 UTC
  • Sudan Ta Kudu : An Yi Zanga-zangar Kin Jinin Amurka A Juba

A Sudan ta Kudu daruruwan mutane ne suka gudanar da wata zanga-zanga jiya Talata, a birnin Juba, domin yin allawadai da matakin Amurka na takaita mika makamai ga kasar.

Masu zanga-zangar dai na kalubalantar matakin da cewa ya saba wa 'yancin da kasar ke da shi, kana wani shiri ne na Amurka na raunana gwamnatin shugaba Salva Kiir.

A ranar Juma'a da ta gabata ne gwamnatin Amurka ta sanar da daukan matakin saboda yawaitar cin zarafi da  muzguna wa fararen hula da ma'aikatan agaji a wannan kasa ta Sudan ta Kudu dake fama da rikici.

Masu zanga zanga sun kuma mika wasu jeri bukatu a ofishin jakadancin na Amurka, kafin daga bisani suka nufi sansanin tawagar kiyaye zaman lafiya na MDD a kasar (Minuss)inda suka yi ta jefe-jefe da duwatsu.