Al'ummar Sudan Na Ci Gaba Da Zanga-Zangar Adawa Da Siyasar Gwamnati.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i28043-al'ummar_sudan_na_ci_gaba_da_zanga_zangar_adawa_da_siyasar_gwamnati.
Al'ummar Sudan Na Ci Gaba Da Zanga-Zangar Nuna Rashin Amincewarsu Da Hauhawar Farashin Kayan Masarufi A Kasar
(last modified 2018-08-22T07:01:24+00:00 )
Feb 08, 2018 14:25 UTC
  • Al'ummar Sudan Na Ci Gaba Da Zanga-Zangar Adawa Da Siyasar Gwamnati.

Al'ummar Sudan Na Ci Gaba Da Zanga-Zangar Nuna Rashin Amincewarsu Da Hauhawar Farashin Kayan Masarufi A Kasar

Tashar Talabijin din France 24 ta habarta cewa hauhawar farashin kayan masarufi da suka hada da alkama na ci gaba fuskantar fishin al'umma a kasar Sudan, da hakan ya janyo cikas a game da siyasar shugaba Umar Al-bashir.

Al'umma kasar a jahohi daban-daban na ci gaba da zanga-zangar nuna adawa da sabuwar siyasar gwamnati a bagaren tattalin arzikin kasar, saidai jami'an 'yan sanda sun kalubalanci masu zanga-zangar tare da yin awan gaba da wasu jagororin 'yan adawa da kuma masu rajin kare hakin bil-adama na kasar.

Tun a farkon makon watan janairun da ya gabata ce, al'ummar kasar ta Sudan suka fara gudanar da wannan zanga-zanga domin nuna adawarsu da sabon kudirin gwamnati a fanin tattalin arzikin kasar.

Ahmad Ta'ib Zainul-Abidin gungu a cikin jam'iyar Democrate ta 'yan adawa ya bayyana cewa bai kamata ba gwamnati ta dage a kan cewa dukkanin kudaden da za ta yi amfani da su a wajen talakawa za a karbo, a daidai lokacin da al'ummar ke cikin matsin tattalin arziki.

'Yan adawar na Sudan sun bayyana cewa za su ci gaba da gwagwarmaya duk kuwa da matsin lambar da take fuskanta daga bangaren gwamnati.