An Yanke Wa Kakakin Madugun 'Yan Tawayen Sudan Ta Kudu Hukumci Kisa
Wata babbar kotu a birnin Juba, babban birnin kasar Sudan ta Kudu ta yanke wa kakakin madugun 'yan tawayen kasar Riek Machar, wato James Gatdet Dak, hukuncin kisa a yau din nan Litinin bayan da kotun ta ce ta same shi da laifin cin amanar kasa da haifar da bore wa gwamnati.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar a yau Litinin ne, babbar kotun da take shari'a wa Mr. James Gatdet Dak ta yanke masa hukuncin kisa saboda samunsa da laifin cin amanar kasa, haka nan da kuma wasu shekaru 21 a gidan maza masu kwadaitar da yin bore da zagon kasa ga gwamnatin shugaba Salva Kiir.
A watan Nuwamban 2016 ne dai gwamnatin Kenya ta mika Mr. Dak wa gwamnatin kasar Sudan ta Kudun lamarin da kungiyoyin kare hakkokin bil'adama da kuma Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da shi saboda a cewarsu hakan ya saba wa dokokin kasa da kasa.
Tsohon Babban lauyan Mr. Dak din Monyluak Alor Kuol, ya ce wannan hukuncin dai ya saba wa yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma.
A halin yanzu dai Madugun 'yan tawayen na Sudan ta Kudu Riek Machar yana tsare a kasar Afirka ta Kudu bayan ya gudu daga Sudan ta Kudu zuwa kasar Kongo. Mahukuntan Afirka ta Kudun dai sun ce suna tsare da shi don haka ne ci gaba da ruruta wutar yaki a kasarsa wacce take cikin yakin basasa tun 2013 bayan da shugaba Kiir din ya kori Mr. Machar daga matsayinsa na mataimakin shugaban kasa inda ya kaddamar da tawaye da nufin kifar da gwamnatin.