Kungiyar CEDEAO Ta Sanya Takunkumi Kan 'Yan Kasar Guine Bisau 19
(last modified Wed, 14 Feb 2018 12:05:42 GMT )
Feb 14, 2018 12:05 UTC
  • Kungiyar CEDEAO Ta Sanya Takunkumi Kan 'Yan Kasar Guine Bisau 19

Kungiyar bunkasa tattalin arzikin yammacin Afirka ta sanya takunkumi kan wasu mutane 19 na kusa da shugaban kasar Guinee Bisau sakamakon rashin mutunta yarjejjeniyar da aka cimma na fita daga rikicin siyasar kasar

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya habarta cewa, wannan takunkumi ya hada da hana su bulaguro gami rufe asusunsu a cikin kasashen dake cikin kungiyar , kuma daga cikin wadanda aka kakabawa takunkumin har da wasu 'yan majalisun dokoki 14 da kuma Dan shugaban kasar Emerson Vaz.

Kafin hakan dai, tun a farkon watan Favrayu, kungiyar ta CEDEAO ta yi gargadin kakaba takunkumi a kan wasu mutane na kasar ba tare da bayyana sunan su sanan a ranar 4 ga watan Favrayu ta sake yin wannan gargadi.

Guinee Bisau, karamar kasa ce dake cikin yammacin kasashen Afirka, kuma ta fada cikin rikicin siyasa ne tun bayan tun bayan da aka yiwa Domingos Simoes Pereira juyin milki a shekarar 2015.