Feb 22, 2019 19:17 UTC
  • Gwamnatin Amurka Ta Yi Barazanar Dorawa Koriya Ta Arewa Takunkumai Masu Tsanani

Sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya bayyana cewa Amurka ba zata dauke takunkuman da ta dorawa Korea ta Arewa ba.

Mike pompoe ya bayyana haka ne wa tashar talabijin ta CBN a yau Jumma'a ya kuma yi barazanar cewa Amurka zata dorawa koriya ta Arewa takunkuman tattalin arziki masu tsanani, wadanda ba zata daukesu ba har sai ta tabbatar da cewa gwamnatin Koriya ta Arewa ta wargaza dukkan shirinta na makaman nukliya. 

Kafin wannan barazanar dai ana saran shugaban kasar ta Amurka Donal Trump zai gana, a karo na biyu da tokoransa na kasar Koriya ta arewa Kim Jong Un, a ranakun 27 da 28 ga watan Febreru da muke ciki a kasar Vetnam.

An gudanar da taro na farko tsakanin shuwagabannin biyu ne a kasar Singapore a ranar 12 ga watan Yunin shekara ta 2018 da ta gabata. 

 A taron na singapore dai shugaban koriya ta Arewa ya yi alkawarin dakatar da shirin kasarsa na makaman Nukliya amma tare da samun lamuni daga gwamnatin Amurka kan wasu al-amura wadanda suka hada da tsaron kasrsa da kuma dauke takunkuman da ta dorawa kasar.

Sai dai daga baya gwamnatin Koriya ta Arewa ta bayyana cewa gwamnatin Amurka bata cika ko da daya daga cikin alkawuran da ta dauka a taron Singapore ba. 

Tags