An Hallaka 'Yan Sandar Kenya Biyu A Kan Iyaka Da Somaliya
Kwamishinan 'yan sanda na yankin arewa maso gabashin kasar kenya ya sanar da mutuwar jami'ansa biyu a wani gumurzu da aka yi a kan iyakar kasar da kasar Somaliya
A cikin wata sanarwa da ya fitar, kwamishinan 'yan sandan yankin arewa maso gabashin kasar kenya Muhammad Saleh ya ce jami'an nasa sun rasa rayukansu ne yayin wani gumurzu da suka yi tsakaninsu da jami'an tsaron kan iyakar kasar da Somaliya.
Muhammad Saleh ya ce 'yan sandan sun yi tunanin cewa jami'an tsaron iyakar kasar, mayakan 'yan ta'addan Ashabab ne ko kuma masu safarar miyagun kwayoyi ne, lamarin da ya sanya suka buda musu wuta.
Kwamishinan 'yan sanda ya kara da cewa wannan lamari ya faru ne a yayin da jami'an 'yan sandar ke kan hanyar su na zuwa garin Mandera dake kusa da kan iyakar kasar Somaliya.
Tun bayan da gwamnatin kasar Kenya ta tura sojojin kasar Somaliya domin yaki da kungiyar Ashabab, yankunan arewa da gabashin kasar suke fuskantar hare-hare daga mayakan na Ashabab.