An Dage Taron Kasashe 3 A kan Madatsar Ruwan Habasha
Ma'aikatar harkokin Wajen kasar Sudan ce ta sanar da dage taron wanda zai kunshi Sudan din da Habasha da kuma Masar.
An shirya cewa daga ranakun 24 zuwa 25 ne za a yi taron na kwararru da injiniyoyi a birnin Khartum. An dage taron ne dai bisa bukatar kasar Habasha kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen Sudan din ta tabbatar.
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Sudan Karibullah al-Khidr ya ce; murabus din da Fira ministan kasar Habasha Hailemariam Desalegn ya yi, yana daga cikin dalilan dage yin taron, sai dai anan gaba za a tsaida lokacin da za a yi shi.
Kasashen Sudan, Masar da Habasha sun kasa cimma matsaya guda akan madatsar ruwan da Habasha ke ginawa wadda ake yi wa lakabi da "Madatsar ruwan Karni"