Rundunar 'Yan Sandan Nijeriya Za Ta Kara Tura Jami'an Tsaro Zuwa Zamfara
Sufeto Janar na 'yan sandan Nijeriya, Ibrahim Idris, ya sanar da cewa nan gaba kadan za a tura karin 'yan sandan kwantar da tarzoma masu yawa zuwa jihar Zamfara don kara karfafa yanayin tsaro a jihar biyo bayan kisan gillan da aka yi a wa wasu mutanen jihar a kwanakin baya.
Sufeto Janar na 'yan sandan ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da yayi da manema labarai a birnin Gusau, babban birnin jihar Zamfaran, inda ya kai ziyarar mika ta'aziyyar harin da aka kai kauyen Birane, da ke karamar hukumar Zurmi na jihar Zamfara da yayi sanadiyyar mutuwar mutane 40 inda ya ce ya kuduri aniyar aikewa da karin 'yan sandan kwantar da tarzoma jihar ta Zamfara.
har ila yau Mr. Idris tuni rundunar 'yan sandan ta kafa wani kwamiti da zai binciko lamari da kuma ba da shawarwari kan yadda za a kawo karshen irin wadannan hare-hare yana mai sanar da cewa gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta amince da daukar 'yan sanda 6,000 don kara karfafa yanayin tsaro a Nijeriyan.
Jihar Zamfaran dai tana ci gaba da fuskantar rikice-rikice da hare-haren wasu mutane da ake zargin barayin shanu ne lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutanen jihar a watannin baya-bayan nan.