An Sallami Wasu Daga Cikin Fursunonin Siyasa A Sudan
Majiyoyin ma'aikatar tsaron cikin gida a Sudan ta sanar da sakin dukkanin fursunonin siyasa da ke kurkukun Kubar da ke birnin Khartum.
Kamfanin dillancin labaran IRNA ya habarta cewa, an dauki matakin sakin fursunonin siyasar ne biyo bayan sake nada Salah Abdullah Muhammad Saleh a matsayin babban daraktan hukumar tsaro ta cikin gida a Sudan.
A ranar 11 ga wannan wata na fabrairu ne shugaban Sudan Umar Hassan Albashir ya sanar da sauke babban daraktan hukumar tsaro ta cikin gida Al-nafiz Muhmmad Ata, ba tare da bayyana wani dalili kan yin hakan ba.
A cikin shekara ta 2009 ne dai Albashir ya sauke Salah Abdullah Muhammad Saleh daga kan wannan mukami ya nada Muhammad Ata, inda kuma yanzu ya sake dawo da shi kan tsohon mukamin nasa.