Wani Dan Kunan Bakin Wake Ya Tarwatsa kansa A Cikin Jami'ar Maiduguri
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i28413-wani_dan_kunan_bakin_wake_ya_tarwatsa_kansa_a_cikin_jami'ar_maiduguri
Majiyar jami'an tsaro a jihar Borno na tarayyar Najeriya ta bayyana cewa wani dan kunan bakin wake ya tarwatsa kansa a cikin jami'ar Maiduguri.
(last modified 2018-08-22T07:01:27+00:00 )
Feb 21, 2018 08:16 UTC
  • Wani Dan Kunan Bakin Wake Ya Tarwatsa kansa A Cikin Jami'ar Maiduguri

Majiyar jami'an tsaro a jihar Borno na tarayyar Najeriya ta bayyana cewa wani dan kunan bakin wake ya tarwatsa kansa a cikin jami'ar Maiduguri.

Kamfanin dillancin labaran Xin Hua na kasar China ya nakalto majiyar jami'an tsaron tana cewa mutum guda ne ya tarwatsa kansa a cikin jami'ar amma babu wata asara ta rai ko ta dukiya in banda na shi dan kunan bakin waken.

Mayakan  boko haram sun dade suna kokarin kutsawa cikin jami'ar ta maiduguri a shekarun da suka gabata, har sun kashe mutate kimani 10 a wani masallacin a cikin jami'ar a shekarar da ta gabata. Har'ila yau a shekarar da ta gabata ma sun kai hari wa tawagar malman jami'a da jami'an tsaro wadanda suke aikin neman mai kusa da tabkin chadi inda suka kashe wasu malaman suka kama wasu.

 Har'ila yau yan matan 94 suka bace bayan wani harin da mayakan na boko haram suka kai kan makarantan yan mata ta Dapchi  a jihar Yobe.