Somaliya: An Sami Karin Wadanda Suka Rasu Sanadiyyar Tashin Bom
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i28509-somaliya_an_sami_karin_wadanda_suka_rasu_sanadiyyar_tashin_bom
Rahotanni daga babban birnin kasar ta Somaliya sun ce adadin wadanda suka rasun ya karu zuwa 18 da kuma wasu 20 da suka jikkata
(last modified 2018-08-22T07:01:28+00:00 )
Feb 24, 2018 03:08 UTC
  • Somaliya: An Sami Karin Wadanda Suka Rasu Sanadiyyar Tashin Bom

Rahotanni daga babban birnin kasar ta Somaliya sun ce adadin wadanda suka rasun ya karu zuwa 18 da kuma wasu 20 da suka jikkata

A jiya juma'a ne dai aka kai tagwayen hare-haren da motocin da aka makare da bama-bamai. Da fari jami'an tsaron kasar sun sanar da mutuwar mutane 3.

Kungiyar 'yan ta'adda ta Al-shabab ta dauki alhakin kai hari,

Shekaru masu tsawo kenan da kasar ta Somaliya take fama da tabarbarewar harkokin tsaro saboda rashin gwamnati mai karfi.

Kungiyar al-shabab tana a matsayin babban kalubalen tsaro ga gwamnatin Somaliya da kuma ta kasashen makwabta.