CAR : An Dage Zaben 'Yan Majalisar Dokoki Zagaye Na Biyu.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i2854-car_an_dage_zaben_'yan_majalisar_dokoki_zagaye_na_biyu.
Hukumar kula da sha'anin zabe a Jamhuriya Afirka ta Tsakiya (ANE) ta sanar da dage zaben cika-maki 'yan majalisun dokokin kasar zagaye na biyu da aka shirya yi ranar Lahadi nan har zuwa ranar 31 ga wata Maris.
(last modified 2018-08-22T06:58:01+00:00 )
Mar 24, 2016 00:57 UTC
  • wata mazaba a Afirka
    wata mazaba a Afirka

Hukumar kula da sha'anin zabe a Jamhuriya Afirka ta Tsakiya (ANE) ta sanar da dage zaben cika-maki 'yan majalisun dokokin kasar zagaye na biyu da aka shirya yi ranar Lahadi nan har zuwa ranar 31 ga wata Maris.

Hakan dai a cewar Marie Madelaine ta hukumar zaben ya biyo bayan tsaiko da aka samu kafin kotun tsarin mulkin kasar ta tantance sakamakon zaben da akayi tun da farko wanda kuma yayi tasiri akan shirye-shiryen zaben a zagaye na biyu.

A cewar jami'ar hukumar idan an ce za'a gudanar da zaben a ranar 27 ga wata to ba za'a samu isashen lokaci ba na isar da kayan zaben a sassan da za'a sake zaben cikin lokaci.

A sakamakon zaben da kotun tsarin mulki kasar ta tantance a ranar 14 ga watan Fabrairu ta amunce da 'yan majalisu 45 cikin 140 da majalisar dokokin kasar ya kamata ta kunsa, inda a yanzu za'a sake zaben a mazabu 85, bayan soke na wasu mazabu 10.

Zaben dai na ranar 31 ga watan idan Allah ya kai ba zasu shafi na wuraren da aka soke ba, wadanda za'a gudanar nan gaba.