Kenya: Zanga-Zangar Nuna Rashin Amincewa Da Cin Zarafin Mata A Kenya
Cincirindon mata ne suka gudanar da wata gagarumar zanga-zanga a birnin Nairobi fadar mulkin kasar Kenya, domin nuna bacin ransu dangane da cin zarafin da suka ce ana yi wa mata a kasar.
Tashar talabijin ta IPTV ta bayar da rahoton cewa, wannan zanga-zanga ta biyo bayan yada wani rahoto ne da ke bayyana yadda aka ci zarafin wasu mata a wasu asibitocin gwamnatin kasar, ba tare da an ladabtar da wadanda suka aikata hakan ba.
Masu zanga-zangar sun bukaci gwamnatin Kenya da ta dauki kwararan matakai a kan duk wanda aka samu da laifin cin zarafin mata a kasar, domin ya zama darasi.
Wannan dai ba shi ne karon farko da ake samun bayanai na cin zarafin mata da keta huruminsu a kasar Kenya ba, ba tare da mahukuntan kasar sun dauki wani mataki ba.