Bankin Raya Afirka Zai Bayar Bashin Dala Biliyan 2 Ga Morocco
Bankin raya Afirka ya sanar da cewa zai bayar da bashin kudi har dalar Amurka biliyan biyu ga Morocco a cikin shekaru biyu, domin gudanar da wasu ayyuka na musamman a kasar.
Mataimakin babban daraktan bankin na Afirka ne Khalid Sharif ya bayyana hakan a jiya, bayan wata ganawa da ya yi da Firayi ministan kasar Morocco Sa'aduddin Al'Usmani a jiya a birnin Rabat.
Khalid Sharif ya ce bayar da wadannan kudade zai taimaka ma kasar Morocco wajen gudanar da wasu muhimman lamurra da za su bunkasa tattalin arzikin kasar, kamar yadda kuma ya ce wasu daga cikin ayyukan na hadin gwiwa tsakanin bankin da kuma gwamnatin Morocco.
Ya kara da cewa cin nasarar wannan shiri a Morocco, zai taimaka wajen aiwatar da shi a wasu kasashen Afirka.