Somaliya : Yawan Mamata Bayan Harin Mogadishu, Ya Kai 32
(last modified Sun, 25 Feb 2018 10:51:29 GMT )
Feb 25, 2018 10:51 UTC
  • Somaliya : Yawan Mamata Bayan Harin Mogadishu, Ya Kai 32

Hukumomin tsaron a Somaliya sun ce, yawan mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon harin Mogadishu, babban birnin kasar ya karu zuwa 32.

Jerin hare haren na ranar Juma'a data gabata, an dai kai na farko ne da wata motar wani waje dake dab da hedkwatar hukumar lekan asiri da tsaro ta kasar Somaliya.

Bayan hakan kuma minti 15, an tayar da wani bom da aka ajiye a wata mota dake kan hanyar zuwa fadar shugaba.

Daga cikin wandanda hare haren suka rusa dasu a cewar hukumomin tsaron kasar, akwai dakaru 5, da kuma wani jami'in tsaro.

Kungiyar Al-Shabaab a Somaliyar ta ce ita ke da alhakin kai jerin hare haren.