Djibouti : Jam'iyya mai Mulki Ta Yi Ikirarin Lashe Zaben 'Yan Majalisa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i28589-djibouti_jam'iyya_mai_mulki_ta_yi_ikirarin_lashe_zaben_'yan_majalisa
Jam'iyya mai mulki ta (UMP) a Djibouti, ta yi ikirarin lashe zaben 'yan majalisar dokokin kasar da aka kada kuri'arsa a ranar Juma'a da ta gabata gagarimin rinjaye.
(last modified 2018-08-22T07:01:29+00:00 )
Feb 26, 2018 07:48 UTC
  • Djibouti : Jam'iyya mai Mulki Ta Yi Ikirarin Lashe Zaben 'Yan Majalisa

Jam'iyya mai mulki ta (UMP) a Djibouti, ta yi ikirarin lashe zaben 'yan majalisar dokokin kasar da aka kada kuri'arsa a ranar Juma'a da ta gabata gagarimin rinjaye.

Jam'iyyar ta Shugaba Ismaël Omar Guelleh, dake shuganacin wannan kasa tun shekara 1999, ta ce ta lashe zaben da kusan kashi 90% na yawan kuri'un da aka kada a zaben da mafi yawan jam'iyyun adawa suka kaurace ma.

Bayyanan da Jam'iyya mai mulki ta UMP ta fitar, sun ce ta samu kujeru 58 cikin 65 na 'yan majalisar dokokin kasar.

Ko a zaben shugaban kasar na 2016 da ya gabata, Jma'iyyar UMP mai mulki ta ci bulus a zaben da 'yan adawa suka kaurace ma, wanda ya baiwa shugaban kasar mai ci, Ismaël Omar Guelleh, yin nasara da kashi sama da 86%.