Shugaban Kasar Sudan Ya Yi Garanbawul Ga Shugabanin Tsaron Kasar
Shugaban kasar Sudan Omar Hassan al-Bashir ya yi garambawul ga shugabannin sojoji da sauran hukumomin tsaro na kasar.
Rahotanni dake fitowa daga kasar Sudan sun tabbatar da cewa a wannan talata, shugaba Omar Hassan al-Bashir na kasar ya Kori babban habsan sojojin kasar Laftanar Janar Emadeddin Adawi daga bakin aiki, Sannan an maye gurbinsa na Laftanar Janar Kamal Abdul Maaruf , ko baya ga hakan Shugaba Hassan al-Bashir ya gudanar da wasu sauye-sauyen ga sauran hukumomi na tsaron kasar ta Sudan da suka hada da hukumar leken asiri.
Wannan mataki da Shugaba al-Bashir ya dauka na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomin kasar Saudiya suka dauki irin wannan mataki a jiya Talatan, inda mahukuntan kasar suka yiwa manyan hafsoshin kasar ritayar karfi, lamarin da masu sharhi ke ganin cewa sauye-sauyen na sudan ba ya rasa nasaba da yakin da kasar saudiya ke yi a kasar yemen ganin cewa kasar ta sudan na daga cikin kawancen saudiya a hare-haren wuce gona da irin da saudiya tare da cikekken goyon bayan Amurka da Turai ke kaiwa kan al'ummar kasar yemen.