Najeriya : An Kafa Kwamitin Binciken Sace 'Yan Makarantar Dapchi
Feb 28, 2018 07:42 UTC
Gwamnatin Najeriya, ta sanar da kafa wani kwamitin da zai binciki hakikanin abunda ya faru kan sace 'yan matan makarantar sakadaren Dapchi dake jihar Jobe a arewa maso gabashin kasar.
Har yanzu dai babu wani labari dangane da 'yan matan su 110 da ake kyautata zaton mayakan boko haram ne suka sace su.
Kwamitin da wani mai babban mukamin soji zai jagoranta, ya kunshi mambobi 12 na Jami'an tsaro da suka hada da sojoji, 'Yan sanda da jmi'an leken asiri da kuma na gwamnatin yankin na Yobe.
Kwamitin zai bada sakamakon bincikensa nan da ranar 15 ga watan Maris mai zuwa, ciki har da gabatar da matakai na hana aukuwar irin wannan lamari nan gaba a cewar ministan yada labarai na kasar Lai Muhammad.
Tags