An Kai Harin Ta'addanci A gefen Babban Birnin Somaliya
(last modified Fri, 02 Mar 2018 18:58:14 GMT )
Mar 02, 2018 18:58 UTC
  • An Kai Harin Ta'addanci A gefen Babban Birnin Somaliya

Majiyar Tsaron Somaliya ta sanar da kai harin ta'addanci a barikin soja dake gefen Magadushu babban birnin kasar

Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa na kasar Sin ya nakalto majiyar tsaron somaliya na cewa 'yan ta'adda kungiyar Ashabab sun tarwatsa wata mota shake da bama-bamai a wani barikin soja dake wajen birnin Magadushu bayan da suka mamaye yankin dake gefen birnin Magadushu.

Majiyar tsaron  ta bayyana cewa nan take bayan kai harin sojojin kasar sun mayar musu da martani, inda suka hallakar daya daga cikin maharan, sannan a bangaren jami'an tsaro, sojoji biyu sun samu rauni sanadiyar kai harin da ake zaton mayakan Ashabab ne suka kai a wannan juma'a.

Saidai a bangare guda, wasu majiyoyin kasar ta Somaliya sun ce sojoji 4 ne suka hallaka yayin da wasu shida na daban suka jikkata sanadiyar harin da kungiyar Ashabab.

A cikin 'yan shekaru baya-bayan nan kasar Somaliya na fuskantar hare-haren kungiyar Al-Shabab, duk da cewa har yanzu kungiyar na rike da wasu yankunan kasar, to amma da taimakon dakarun wanzar da zaman lafiya na kasashen Afirka, hukumomin kasar na ci gaba da jan ragamar jagorancin kasar.