Zanga-Zangar Adawa Da Cin Zarafin Mata A Kenya
(last modified Fri, 02 Mar 2018 19:02:19 GMT )
Mar 02, 2018 19:02 UTC
  • Zanga-Zangar Adawa Da Cin Zarafin Mata A Kenya

Dariruwan matan kenya sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da yadda ake cin zarafinsu a Nairobi babban birnin kasar

Rahotani dake fitowa daga birnin Nairobi na kasar Kenya sun tabbatar da cewa dariruwan matan kasar ne suka fito kan titinan birnin domin nuna fishinsu kan yadda ake ci gaba da cin zarafin mata a kasar, inda suka bukaci gwamnati ta dauki mataki na yadda za a kawo karshen wannan mumunar dabi'a a fadin kasar gaba daya.

Matan na kenya sun tabbatar da ci gaba da gwagwarmaya har sai sun tabbatar da dawo musu da martabar su da kuma hakkokinsu a kasar.

Mahalarta zanga-zangar sun ce mata a kasar ta kenya suna fuskantar cin zarafi har ma da yi musu fyade a yankunan da masu karamin karfi suke rayuwa, kuma sun ce a cikin 'yan shekarun nan wannan mumunar dabi'a sai kara habbata take a kasar domin haka ya zama wajibi su tashi tsaye domin ganin sun kwatowa kansu 'yan ci a kasar.