Sudan Da Masar Sun Sake Kulla Dangantar Diflomatsiyya
Kasashen Sudan da Masar sun sanar da sake kulla huldar diflomatsiyya a tsakaninsu, a cewar ministan harkokin wajen Sudan.
A ranar Litini mai zuwa ce Sudan za ta sake bude ofishin jakadancinta a Masar, a cewar ministan harkokin wajen kasar ta SUdan, Ibrahim Ghandour.
Wannan matakin dai na zuwa watanni biyu bayan da Sudan ta janye jakadanta a Masar biyo bayan takaddamar data kunno tsakanin kasashen biyu.
Tun da farko dai ba'a bayyana wane irin sabani ne ba ya haifar da tsamin dangantaka tsakanin kasashen biyu, amma a yanzu a cewar ministan harkokin wajen kasar ta Sudan, bangarorin biyu na da hakkin su martaba dadadiyyar hulda da tarihi dake tsakaninsu.
Ko da yake mahukuntan Khartoum basu fayyace dalilin janye jakadan nasu a waccen lokacin, amma ana ganin takadamar bata rasa nasaba da yankin nan na Halayeb da bangarorin biyu ke takkadama a kai.