Yiwa Mata Masu gwagwarmaya fyade a kasar Sudan
Ana zarkin Dakarun tsaron Sudan da yiwa Mata 'yan gwagwarmaya fade a kasar
Kamfanin dillancin Labaran Kasar faransa ya naklto wata majiyar kasar Sudan da ta bukaci a sakaye sunanta a yau Alkhamis na cewa jami'an tsaro na ofisoshin leken asirin kasar da azabtar da 'yan adawar Gwamnati tare da na kungiyoyin kare hakin bil-adama a kasar kuma idan suka kame Mata daga cikin su na yi musu fade.
Wanan labari ne na zuwa ne a yayin da kungiyar kare hakin bil-adama ta duniya ta fitar da wani rahoto na cewa Mata 'yan gwagwarmaya da masu rajin kare hakin bil-adama a kasar ta sudan na fuskantar matsalar cin zarafi da kuma fade daga jami'an tsaron kasar, inda ta fitar da wani kundi mai dauke da hujjoji na wannan batu.har ila yau kungiyar ta ce wasu mata 'yan gwagwarmaya da dama ne suka fuskanci wannan barazana daga bangaren jami'an tsaron kasar ta Sudan.kuma abin mamaki shi ne har yanzu babu wani jami'in tsaro guda da aka bincika dangane da wannan zarki.
Wannan barazana ne dai ta sanya diyawa daga cikin Mata na kasar Sudan barin kasar ta su ko kuma rufe bakunansu domin kaucewa wannan lamari.
Saidai Gwamnatin Khartum ta yi watsi da wannan zarki.