Al'Shabab Ta Kashe Sojin Somaliya Hudu
Mar 03, 2018 16:12 UTC
Wani harin kunar bakin da aka kai da mota a wani barikin soji a arewa maso gabashin Mogadisho, ya yi ajalin wani sojin Somaliya guda.
A cewar rubndinar sojin kasar, kungiyar Al'shabab ce ta kai harin na JIya Juma'a.
A cewar kwamandan rundinar sojin kasar, an kai harin ne a lokacin da ba kowa a barikin sojin.
A wani labari kuma, kakakin sojin kasar ya ce, sojoji uku ne suka rasa rayukansu a wani harin kwantan bauna da aka kan tawagar sojojin Burundi a tsakanin Mogadisho zuwa Jowhar.
Kungiyar ta Al'shabab ta bakin kakakinta, ta shaidawa kamfanin dilancin labaren Reuters cewa mayakansu sun kwace iko da birnin Balad dake nisan kilomita talatin a arewacin Mogadisho babban birnin kasar.
Tags