Zambiya Ta Kori Baki 47 Daga Cikin Kasar
Ma'aikatar 'yan gudun hijra ta kasar Zambiya ta sanar da korar baki 47 dake zaune a kasar ba kan ka'ida ba
Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa na kasar Sin ta nakalto ma'aikatar dake kula da 'yan gudun hijra ta kasar Zambiya cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya litinin , ta ce daga cikin baki 47 da ta kora daga cikin kasar 46 'yan kasar Ethiopia ne.
Sanarwar ta ce kafin a hukunta mutanan, sun kwace watani a gidan kaso, kuma kotun kasar ta umarci a fitar da su daga cikin kasar saboda ta same su da laifin shiga kasar ba bisa ka'ida ba.
A watan Oktoban shekarar 2017 din da ta gabata ce, jami'an 'yan sandar Zambiya suka sanar da cewa sun cabke 'yan kasashen waje 71 da suka shiga kasar ba kan ka'ida ba, kuma daga cikin su 46 'yan kasar Habasha ne.
Rahoton ya ce daga cikin bakin da ake tsare da su har da 'yan kasar Faransa.